Ina ba da gaskiya ga Allah uba Mai iko duka. Mai halitar sama da kasa. Ina ba da gaskiya ga Yesu kristi Dansa makadaici Ubangijinmu, wanda aka habila ta wurin Ruhu mai Tsarki, haifuwa tasa daga budurwa Maryamu, Ya sha wahala cikin zamanin Bilatus Babunte, aka giciye shi, Ya mutu, aka bizne shi, Ya tafi Hades: Rana ta uku ya tashi kuma daga matattu, Ya hau bisa cikin sama, yana zaune ga hannun dama na Allah Uba Mai iko duka; Daga can za shi zuwa garin Ya yi shari’a bisa masu rai da matattu. Ina ba da gaskiya ga Ruhu Mai Tsarki; Ekklesiya mai Tsarki Katolika; Zumuntar Tsarkaka; Gafarar zunubai, tashin jiki, da rai mara matuka. Amin.